M.I Abaga ya saki jerun wakokin sabon kundin da yake shirye-shiryen sakewa mai taken Yung Denzl. Bayan tsawon lokacin da ya dauka yake daga lokutan sakin fefen, M.I ya bayyana a shafin san a Instagram cewa sabuwar ranar ita ce ranar 18 ga watar Agusta, 2018. Fefen da zai kunshi wakoki goma (10) yana dauke da wakar “Rappers should fix up your life” wanda ya jawo banbance-banbancen ra’ayoyin mawaka masu salon rap a duniyar mawaka. Jerin mawakan da zasu fito a cikin kundin su kunshi Niyola, Yay Iwar, Odunsi the Engine, Lady Donli da dai sauran su. Akwai jerun makada wadanda suka yi aiki a kan fefen irin su Tay Iwar, Chopstix, MajorBangz, Doz, GClef, MI Abaga da kan sa da dai sauran su.