Shirin Socio-economic Rights and Accountability Project (SERAP) ta yi
kira ga Hukumar Watsa Shirye-shiry ta
kasar Najeriya (NBC) da ta sauki hukuncin da ta dauka ga wata kafar yada
labarai saboda laifin saka wakokin wasu mawaka irin su This is Nigeria wanda
Falz ya rera, Iskaba wanda Wande Coal ya rera da kuma Wakar See Mary, See Jesus
wanda Olamide ya rera.
Kungiyar ta bayanna cewa wannan
hukuncin da hukumar ta dauka ta saba da dokar kasa wanda ta ba wa gidajen radio
wani yanci na bayanna abubuwan da ke damun talakawan kasa, yancin fadar
albarkacin bakin su da kuma yancin bayyana ra’ayoyin su.
A wata sanarwa da SERAP ta fitar da
ta bakin Mataimakin Shugaban na kungiyar, Timothy Adewale ya ce “damuwar mu
game da hukuncin da NBC ta dauka a kan wannan gidan radio da kuma wakokin wanda
suke yunkurin cewa suna cike da sakin layi da almubazzaranci, yana nuni da cewa
talaka bashi da wani yanci game da bayyana damuwar sa.
Saboda haka, NBC su dage
wannan danyen hukuncin da suka dauka a kan wannan gidan radio kuma su janye
tarar da aka ce zasu biya.
Comments