Beyonce
ta bayyana cewa wajibi ne ta taimaka wa mawaka masu tasowa.
A
makon da ya gabata, labarai ya nuna cewa Tyler Mitchell mai shekaru 23 a duniya
itace mace na farko mai launin bakir fata wadda za ta fara daukar hoto a
mujallar Vogue wace Beyonce ce tauraruwar da aka gayata.
Beyonce ta ce “sai mun hada kawunan
mu mun zamto tsintsiya madaurin ki daya, nuna wariyar launin fata sam bai
kamata ya zamo abin da zai jawo mu tsani juna ba. Wannan shi ne dalilin da ya
sa na ce zan yi aiki tare da mai daukan hota dake da shekaru 23.”
“A lokacin da na fara shekaru 21 da
suka gabata, an gaya min cewa da wuya mai launin bakir fata ya samu hoton kan
sa a shafin farko na mujallar saboda masu bakir fata ba sa jawo kasuwa. Amma
wannan duk camfi ne.”
“Kowa na bukatan wani dama a rayuwar shi. Akwai mata da dama wadanda suka samu dama kafin ni. Irin su Josephine Baker, Nina Simone, Eartha Kitt, Aretha Franklin, Tina Turner, Diana Ross, Whitney Houston da dai sauran su. Su suka buda min kofa, kuma ina fatan ni ma zan yi iya bakin kokari na domin na bude wa wadanda Allah yayi musu wata baiwa ta musamman.

Comments