Shahararen mawakin salon hiphop a Najeriya Illbliss ya bayyana wulakancin
da ya sha a hannun SpecialAnti-Robbery Squad wanda ake yawaita kiran su da
sunan SARS.
Mawakin ya rubuta a shafin twitter cewa ma’aikatan SARS sun sa mar
bindigogin su a kan sa bayan da suka caje shi a kan zargin sa da suke cewa yana
dauke da tramadol, wa kwayar da gwamnatin najeriya ta dakatar sabo da yawan
shan sa da matasa suke yi.
Irin wadannan hargitsi da cin
mutuncin da ake nuna wa jama’a shi ya kawo zangazanga wanda ake a shafin sada
zumunci da hashtag ENDSARS kusan shekara dayaa yayin da jama’a suke kiranye da
a gyara al’amurorinsu ko a sauke su daga ragamar aikin su domin irin wulakanta
jama’an da suka sai kace barayi aka kama.
Ire-iren wadannan abubuwan ya sha
faruwa da mawaki da dama a kasar yayin da suke fuskantar wulakanci daga jami’an
tsaro. Yawanci, ana zargin su da zamba saboda nuna irin pacakan da suke da
arziki a idon jama’a. Akwai wadanda basasamun daman bayyana abun da ya faru da
su bayan haduwar da jami’an SARS sai dai a ji labara daga bakin abokan arziki
koi don masu kalo a wannan lokacin.
Comments