Bayan hukuncin da Hukumar watsa shirye-shirye ta kasa ta yanke game da
wakar This is Najeriya wanda Falz ya saka, mawakin ya bayyana rashin jin dadin
shi game da wannan hukuncin da hukumar ta dauka.
Falz ya rubuta a shafin sa na sada zumunci wato twitter cewa “Wannan it
ace Najeriya. Duba yanda muke zama yanzu, kowa ya zama mailaifi” sun ce na yi sakin
layi.” Bayan da ya yada hoton wasikar dake dauke da wannan sanarwa.
Sanannun mawaka da masu alaka da wasan kwaikwayo da fina-finai irin su Kemi Adetiba, Abimbola Craig, Simi, Yemi Alade, Vector da dai sauransu, sun mayar da martini game da wannan danyan hukuncin da suke ganin hukumar ta dauka.

Wannan dai ba shi ne karo na farko
kenan da wakar ta samu suka daga bangaren hukumar ba domin kungiyar Muslim
Rights Concern (MURIC) sun taba kawo korafi da Falz ya janye wakar ko ya
fiskanci hukunci a kotu. A bayanin su, sun yi korafi ne domin cin mutuncin
hijabin da mawakin yayi bayan da wasu yan mata suna rawan shaku-shaku lulube
cikin hijabi.
Comments