Tsohon jarumin mawakin hiphop na kasar amurka, Ice-cube ya kara jadadda bayanin furucin da yayi dangane da maganar da yayi akan mawakin da yake fice a halin yanzu, wato Drake.
A wani tattaunawar da aka yi da shi a wani shiri, tsohon attajirin mawakin ya ce duk wani mawaki yana da wa’adi na shekaru a cikin harkar waka wanda zai samu daman shanawa. Bayan haka kuwa, yayin sa dole ne ya wuce domin abune wanda ya saba gani yana faruwa da mawaka da dama.
“Ba wai maganar da nayi ya shafi Drake bane kadai, a cewar sa. Wannan ra’ayi na ne game da harkar waka. Yawanci mawaki kan yi tashe daga shekaru uku, watakila zuwa biyar kafun masana’antar ta fara neman wani sabon abu. Haka na gan yake faruwa domin ya faru da ni."
"Bayan tashen shi mawakin, ya zama dole shi mawakin ya samu inda zai dauwama a cikin harkar. Kar dai ka sake ka durkushe ga baki daya a cikin harkar. Kai dai ka samu wani wuri ka fake, ka cigaba da sarrafa wakoki, ka cigaba da tara masoya. Wannan shine jawabin bincike na, ba wai suka ne ga Drake ba.”Da suka tambaye shi ko waye ya ke tashe a halin yanzu? Sai yayi murmushi yace “Ban sani ba domin wannan baya gaba na. Abun da na fi damuwa da shi shine, wai shin yaya salon wakar mawakin yake. Idan wakar na da ma’ana kuma ya hadu, dole na so shi. Idan babu wani ma’ana, tabas bazan so shi ba. Saboda haka, idan mawaki na wakoki masu ma’ana, a ra’ayi na kai babban mawaki ne. Idan kuwa wakokin ka basu da ma’ana, tabbas baka layi na.
Comments