Nicki Minaj
ta saki sabon fefen ta mai taken QUEEN wato Sarauniya. Minaj ta saki aikin ne
bayan da ta sanar a shirin Beats 1 Radio Show cewa ta gama aikin a yini uku
kafin zuwan ta shirin.
Aikin na kunshe ne da manyan mawaka irin su Eminem, The
Weeknd, Lil Wayne, Ariana Grande, Future, Swae Lee, Labrinth da kuma tsohuwar
mawakiyar salon rap wato Foxy Brown.
Sabon Fefen ya samu dan tangarda bayan da aka canza lokacin
sakin aikin har sau biyu duba da yar mishkilar da aka samu tare da takwararta
Ariana Grande amma tuni aka warware wannan matsalar.
Comments