A kwanakin baya da suka wuce, mawakiyar kasar amurka Ciara ta saki
sabuwar waka wadda ta rera tare da mawakin najeriya mai sunan Tekno mai taken
Freak Me bayan kusan shekaru uku da yi murabus.
Masoya basu boye mamakin su ba
ganin salon wakar yayi kamancance da irin wakar da mawakiyar kungiyar mavins
record Tiwa Savage ta rera mai taken “Before Nko”.
Mawakiya Ciara wace ta taba lashe
kyautar kambun Grammy ta rubuta a shafi ta na twitter cewa Tiwa ta na daya daga
cikin marubutan wakar domin ita ce ta jawo hankalin ta game da irin wakar salon
Afro-pop.
Ciara ta jaddada cewa a lokacin da
ta fara jin wakar, ta matukar so lafazi da salon wakar shiyasa ta gayace Tiwa
Savage ta bayar da ta ta gudumuwar ta bangaren rubuta wakar tare da ita.
Comments