Niniola ita ce mawakiyar farko da ta fara ajiye tarihi a yayin da ta zama
macen da ta samu masu sauraro miliyan daya a dandamalin Spotify.
Mawakiyar mai salon AfroHouse ta
saki fefen wakar ta mai taken THIS IS ME a watar Nuwamba 2017, ta shawo kan
masana a yayin da wakar ta mai taken Maradona ke kan gaba da masu sauraro sama
da miliyan daya da digo bakwai a shafin dandamalin Spotify.
Dandamalin da ke dora wakokin
mawaka wanda yake auna daukakar mawaki ta hanyar yawan masu sauraro sun tabatar
da wanan nasarar da ta samu a yayin da suka karrama ta da kyautar “macen da ta
fi kowa fice a najeriya”.
Niniola mawakiya ce, kuma
marubuciyar wakoki ce mai muryar zinariya, ta kirkiri wani salon na karan kanta mai taken AfroHouse, wani salo da ke
kunshe da salon AfroBeat da House music.
Comments