Hukumar watsa shirye-shirye ta Najeriya NBC sun dakatar da wakar Folarin
Falana wanda aka fi sani da sunan Falz a yayin da suka saki wata wasika mai
kunshe da wannan gargadin.
Idan za a tuna a baya, hukumar ta
dakatar da gidajen radio da talabijin da su dakatar da saka wakar THIS IS
NIGERIA domin wakar na kunshe da sakin layin da mawaki Falz ya rera dangane da
yanayin da kasar Najeriya take ciki.
A wasikar, an dakatar da wakokin
Olamide mai taken See mary, See Jesus da kuma Wakar Wande Coal mai taken
ISKABA.
Hukumar ta kara da cewa sabo da
sabawa dokokin da gidan yada shirye-shiryen ya yi, an caje shi naira dubu 100 a
matsayin tarar da za a biya.
Comments