Shahararen mawakin salon hiphop a Najeriya Illbliss ya bayyana wulakancin da ya sha a hannun SpecialAnti-Robbery Squad wanda ake yawaita kiran su da sunan SARS. Mawakin ya rubuta a shafin twitter cewa ma’aikatan SARS sun sa mar bindigogin su a kan sa bayan da suka caje shi a kan zargin sa da suke cewa yana dauke da tramadol, wa kwayar da gwamnatin najeriya ta dakatar sabo da yawan shan sa da matasa suke yi. Irin wadannan hargitsi da cin mutuncin da ake nuna wa jama’a shi ya kawo zangazanga wanda ake a shafin sada zumunci da hashtag ENDSARS kusan shekara dayaa yayin da jama’a suke kiranye da a gyara al’amurorinsu ko a sauke su daga ragamar aikin su domin irin wulakanta jama’an da suka sai kace barayi aka kama. Ire-iren wadannan abubuwan ya sha faruwa da mawaki da dama a kasar yayin da suke fuskantar wulakanci daga jami’an tsaro. Yawanci, ana zargin su da zamba saboda nuna irin pacakan da suke da arziki a idon jama’a. Akwai wadanda basasamun daman bayyana abun da ya fa