Skip to main content

Posts

MI ya saki jerin kundin sabon fefen sa mai taken Yung Denzl

M.I Abaga ya saki jerun wakokin sabon kundin da yake shirye-shiryen sakewa mai taken Yung Denzl. Bayan tsawon lokacin da ya dauka yake daga lokutan sakin fefen, M.I ya bayyana a shafin san a Instagram cewa sabuwar ranar ita ce ranar 18 ga watar Agusta, 2018. Fefen da zai kunshi wakoki goma (10) yana dauke da wakar “Rappers should fix up your life” wanda ya jawo banbance-banbancen ra’ayoyin mawaka masu salon rap a duniyar mawaka. Jerin mawakan da zasu fito a cikin kundin su kunshi Niyola, Yay Iwar, Odunsi the Engine, Lady Donli da dai sauran su. Akwai jerun makada wadanda suka yi aiki a kan fefen irin su Tay Iwar, Chopstix, MajorBangz, Doz, GClef, MI Abaga da kan sa da dai sauran su.

Zan cigaba da taimaka wa mawaka masu tasowa inji Beyonce

Beyonce ta bayyana cewa wajibi ne ta taimaka wa mawaka masu tasowa. A makon da ya gabata, labarai ya nuna cewa Tyler Mitchell mai shekaru 23 a duniya itace mace na farko mai launin bakir fata wadda za ta fara daukar hoto a mujallar Vogue wace Beyonce ce tauraruwar da aka gayata. Mujallar da za ta shige kasuwa a watan Satumba za a samu a kasuwani da dama. Beyonce ta ce “sai mun hada kawunan mu mun zamto tsintsiya madaurin ki daya, nuna wariyar launin fata sam bai kamata ya zamo abin da zai jawo mu tsani juna ba. Wannan shi ne dalilin da ya sa na ce zan yi aiki tare da mai daukan hota dake da shekaru 23.” “A lokacin da na fara shekaru 21 da suka gabata, an gaya min cewa da wuya mai launin bakir fata ya samu hoton kan sa a shafin farko na mujallar saboda masu bakir fata ba sa jawo kasuwa. Amma wannan duk camfi ne.” “Kowa na bukatan wani dama a rayuwar shi. Akwai mata da dama wadanda suka samu dama kafin ni. Irin su Josephine Baker, Nina Simone, Eartha Kitt, Are...

Tiwa Savage ita ce ta janyo hankali na game da salon Afropop inji Ciara

A kwanakin baya da suka wuce, mawakiyar kasar amurka Ciara ta saki sabuwar waka wadda ta rera tare da mawakin najeriya mai sunan Tekno mai taken Freak Me bayan kusan shekaru uku da yi murabus. Masoya basu boye mamakin su ba ganin salon wakar yayi kamancance da irin wakar da mawakiyar kungiyar mavins record Tiwa Savage ta rera mai taken “Before Nko”. Mawakiya Ciara wace ta taba lashe kyautar kambun Grammy ta rubuta a shafi ta na twitter cewa Tiwa ta na daya daga cikin marubutan wakar domin ita ce ta jawo hankalin ta game da irin wakar salon Afro-pop. Ciara ta jaddada cewa a lokacin da ta fara jin wakar, ta matukar so lafazi da salon wakar shiyasa ta gayace Tiwa Savage ta bayar da ta ta gudumuwar ta bangaren rubuta wakar tare da ita.

Nicki Minaj ta saki sabon fefe mai taken QUEEN

Nicki Minaj ta saki sabon fefen ta mai taken QUEEN wato Sarauniya. Minaj ta saki aikin ne bayan da ta sanar a shirin Beats 1 Radio Show cewa ta gama aikin a yini uku kafin zuwan ta shirin. Aikin na kunshe ne da manyan mawaka irin su Eminem, The Weeknd, Lil Wayne, Ariana Grande, Future, Swae Lee, Labrinth da kuma tsohuwar mawakiyar salon rap wato Foxy Brown. Sabon Fefen ya samu dan tangarda bayan da aka canza lokacin sakin aikin har sau biyu duba da yar mishkilar da aka samu tare da takwararta Ariana Grande amma tuni aka warware wannan matsalar. Aikin na kunshe da wakoki goma sha tara bayan da ta saki wakoki uku kamun sakin aikin.Wakokin da ta saki tun da fari su ne “Barbie Thinz”, “Chun Li” da “BED”.

Spotify ta karrama mawakiya Niniola

Niniola ita ce mawakiyar farko da ta fara ajiye tarihi a yayin da ta zama macen da ta samu masu sauraro miliyan daya a dandamalin Spotify. Mawakiyar mai salon AfroHouse ta saki fefen wakar ta mai taken THIS IS ME a watar Nuwamba 2017, ta shawo kan masana a yayin da wakar ta mai taken Maradona ke kan gaba da masu sauraro sama da miliyan daya da digo bakwai a shafin dandamalin Spotify. Dandamalin  da ke dora wakokin mawaka wanda yake auna daukakar mawaki ta hanyar yawan masu sauraro sun tabatar da wanan nasarar da ta samu a yayin da suka karrama ta da kyautar “macen da ta fi kowa fice a najeriya”. Niniola mawakiya ce, kuma marubuciyar wakoki ce mai muryar zinariya, ta kirkiri wani salon na karan   kanta mai taken AfroHouse, wani salo da ke kunshe da salon AfroBeat da House music.

SARS sun kusa hallaka ni inji Illbliss

Shahararen mawakin salon hiphop a Najeriya Illbliss ya bayyana wulakancin da ya sha a hannun SpecialAnti-Robbery Squad wanda ake yawaita kiran su da sunan SARS. Mawakin ya rubuta a shafin twitter cewa ma’aikatan SARS sun sa mar bindigogin su a kan sa bayan da suka caje shi a kan zargin sa da suke cewa yana dauke da tramadol, wa kwayar da gwamnatin najeriya ta dakatar sabo da yawan shan sa da matasa suke yi. Irin wadannan hargitsi da cin mutuncin da ake nuna wa jama’a shi ya kawo zangazanga wanda ake a shafin sada zumunci da hashtag ENDSARS kusan shekara dayaa yayin da jama’a suke kiranye da a gyara al’amurorinsu ko a sauke su daga ragamar aikin su domin irin wulakanta jama’an da suka sai kace barayi aka kama. Ire-iren wadannan abubuwan ya sha faruwa da mawaki da dama a kasar yayin da suke fuskantar wulakanci daga jami’an tsaro. Yawanci, ana zargin su da zamba saboda nuna irin pacakan da suke da arziki a idon jama’a. Akwai wadanda basasamun daman bayyana abun da ya fa...

Dr Sid shine musabbabin rabuwar Mohits

Rabuwar shahararen kungiyar MO’hits an yi zaton cewa Dr Sid shine musababbin rabuwan kawunan yayan kungiyar.  Ana ta alwashin cewa Dr Sid na kishin daukakar da Dbanj ya samu a matsayin mai jagoran kungiyar. Bayan hira da manema labarai, Dr Sid ya kara jadadda cewa sam ba haka bane. A cewar sa “Wannan labarin kanzon kurege ne. Bani da wani dalilin da zai sa in nuna kishi na ga   D’banj. Duk abubuwan da muke yi tamkar yan uwa daya muke. Idan har ina da wani damuwa da shi, kai tsaye zan same shi domin mu warware matsalar da ke tsakanin mu. Ban so rabuwar kungiyar Mo’hits ba amma akwai abubuwan da ya fi karfin mu. Farin ciki na shine kowa ya samu cigaba a harkokin sa”.