Mashahuriyar mawakiya Rihanna wanda asalin sunan ta Robyn Fenty ce, ta zama hamshakiyar attajira. Jaridar Forbes ne suka tabbatar da hakan bayan da suka bayyana cewa dukiyar Rihanna ya kai kimanin biliyan $1.7 wanda wannan ke nunin cewa ita ce kan gaba a jerin hamshaken attajirai da tafi kowa yawan arziki a fannin mawaka mata. Sannan kuwa ta zama itace ta biyu a cikin jerin hamshaken mata masu arziki a fannin nishadi bayan Oprah Winfrey. Yanzu Rihanna ta shafa shekaru biyar kenan tun da ta saki kundin fefen wakar ta mai sunan "Anti" wanda ta samu gurbi a cikin jerin kundin wakokin Billboard har satika 63. Ta dau wannan tsawon lokacin ne wurin fadada harkar kasuwancin ta mai sunan Fenty Beauty wanda kamfani ne na kayan kwalliyan mata da kuma kamfanin Savage X Fenty wanda kamfani ne na kamfai irin na mata. Jaridar Forbes sun kiyasta dukiyar ta na Fenty Beauty ya kai kimanin dalla biliya 2.8. A shekarar 2018 lokacin da aka fara gudannar da cinikayya, kamfanin ya sa