Skip to main content

Mr 442 da Ola of Kano na tsare a gidan maza dake kasar Nijar

Hukumomin kasar jamhuriyar Nijar sun ce sun fara bincike kan yadda mawakan nan biyu 'yan Najeriya suka mallaki takardun kasar na bogi da aka kama su da su.

Babban mai shigar da kara na kasar ya ce babban laifi ne yin amfani da takardun bogi a jamhuriyar Nijar , ya kara da cewa sun bayar da umarni a gudanar da bincike domin gano hakikanin gaskiya game da lamarin.

Ya ci gaba da cewa ''Duk wanda aka samu da laifi za mu tasa keyarsa zuwa gaban kotu, ba za mu yadda wasu su rika amfani da takardun kasarmu ta hanya wadda take ba ta gaskiya ba, kuma nan gaba duk wanda aka kama da irin wannan laifin to ya kuka da kanshi''.

To sai dai kungiyoyi masu rajin kare hakkin bil adama sun fara kiraye-kirayen a bincika domin gano yadda aka yi mawakan suka samo takardun zama 'yan kasar, kasancewar sun samo takardun ne a wasu wuraren kafin su zo wajen da za a yi musu fasfo, tare da kiran a yi musu adalci kamar yadda shugaban muryar Talaka na Jamhuriyar Nijar Alhaji Nasiru Saedu ya shaida.


Babban mai shigar da karar ya yi watsi da rade-radin da ake yadawa cewa ana neman belinsu kan sefa (CFA) ta nijar miliyan 10, yana mai cewa har yanzu babu wata takarda da ke nuna hakan da ta zo gabansa, kuma a cewar sa idan ma ta zo, to hakan ba zai taba tabbata ba sai da amincewarsa ko akasin haka.

A yanzu haka dai ana ci gaba da tsare Mubarak Abdulkareem wanda aka fi sani da 442 da manajansa Orler Of Kano a gidan yarin birnin Yamai inda suke zaman jiran kammala bincike kamar yadda babban mai shigar da kara na gwamnati ya shaidawa manema labarai.

Comments

Popular posts from this blog

BILLY O - KATAKO

After remaining a legend in the music game for more than a decade, Billy O finally release the smashing single titled KATAKO. KATAKO is a song with a mixed meaning. Though Katako means Timber in English language, this song is more of  a proverbial song that has a deep meaning lying in it. The afro-centric rhythm of the song will make you love the unique style re-created by BILLY O and as a matter of fact, he knows how to deliver when he meets the best. Produced by Nexcezz Beatz, download and listen to this sumptous tune by BILLY O titled KATAKO . BILLY O - KATAKO mp3

RICQY ULTRA -TSAYA KAJI

RICQY ULTRA IS ONE OF THE FEW EMCEES IN KANO CITY WHO ARE STICKING THEIR GUNS TO THE REAL HIP-HOP CULTURE. AFTER CHURNING AND DROPPING SINGLES, MIXTAPES AND VIDEOS PORTRAYING THE VIBRANT HIP-HOP CULTURE IN NORTHERN NIGERIA, HE UNLEASHES THIS BRAND NEW JOINT TITLED "TSAYA KAJI" . "Tsaya Kaji" is a Hausa word which means "Just Listen" is a strong hip-hop sound that has a deep energy. The song is a conscious rap song which resonates elements like boldness, courage, envy, hate, pain and authority. The lyrical delivery from verses laid in the song tells a lot of story. Verse 1 of the song tells a story about how the patient ones are being taken for granted and treated like slaves, how you can hardly trust friends and  everyone around you is so unpredictable. Verse 2 summarises a tale of a young boy whose parents are poor and visibly sick. He left them for Almajiranci to Kano city to hustle only to meet people with the same fate as he. What next? ...