Hukumomin kasar jamhuriyar Nijar sun ce sun fara bincike kan yadda mawakan nan biyu 'yan Najeriya suka mallaki takardun kasar na bogi da aka kama su da su. Babban mai shigar da kara na kasar ya ce babban laifi ne yin amfani da takardun bogi a jamhuriyar Nijar , ya kara da cewa sun bayar da umarni a gudanar da bincike domin gano hakikanin gaskiya game da lamarin. Ya ci gaba da cewa ''Duk wanda aka samu da laifi za mu tasa keyarsa zuwa gaban kotu, ba za mu yadda wasu su rika amfani da takardun kasarmu ta hanya wadda take ba ta gaskiya ba, kuma nan gaba duk wanda aka kama da irin wannan laifin to ya kuka da kanshi''. To sai dai kungiyoyi masu rajin kare hakkin bil adama sun fara kiraye-kirayen a bincika domin gano yadda aka yi mawakan suka samo takardun zama 'yan kasar, kasancewar sun samo takardun ne a wasu wuraren kafin su zo wajen da za a yi musu fasfo, tare da kiran a yi musu adalci kamar yadda shugaban muryar Talaka na Jamhuriyar Nijar Alhaji Nasir...