Baba Chinedu ya aikawa mai girman gwamnan jihar Kano, Alhaji Abdullahi Umar Ganduje wata budadiyar wasika wanda ke kunshe da jawabi game da kayan dakin da aka yi alkawarin kawowa amma ba a cika alkawarin ba tun shekarar 2018.
A jawabin da Baba Chinedu yayi, ya bayyana cewa tabbas Mai girma gwamna ya turo kayan daki da darajar su ta haura miliyan biyar (5,000,000:00) amma kayan basu isa gidan shaharen dan wasa marigayi Rabilu Musa wanda aka fi sanin sa da Dan Ibro ba bayan da aka daura wa 'yar sa aure.
Kunshe a cikin wasikar, kayan dakin sun biyo ne ta ofishin mai kula da tantance fina-finai da dab'i ta jihar Kano wanda aka fi sanun su da sunan Kano Censorship Board, Alh. Isma'ila Afakallah. Alh. Afakallah a wannan lokacin ya saki hotunan kayan a shafin sa na Instagram amma asali, kayan basu isa gidan Ibro ba har yanzu.
Baba Chinedu ya bayyana cewa sanda aka siyar da daya daga cikin gidajen marigayi Ibro kamun aka biya kayan da aka karba wanda kudadden su kai kimanin dubu dari bakwai. Bugu da kari, an samu cece-kuce tsakanin iyalan Marigayi Ibro da wadanda suka auri 'yar sa game da kayan dakin.
Domin kallo/saukar da wannan bidiyo, latsa nan
Comments