Mashahurin mawakin dan kasar Ghana Sarkodie ya shigar da sunan sa cikin kundin tarihi a yayin da ya zamo mutumin farko da ya fara lashe kundin Best International Flow act a taron BET Hip-hop Awards na 2019.
Taron kambawar wanda aka gudanar a Cobb Energy Performing Arts Center dake Georgia a kasar Amurka, Sarkodie shi ya zama gwarzo a wannan rukuni. Akwai mawaka irin su Falz The BadGuy daga kasar Najeriya, Ghetts daga kasar Ingila, Kalash daga kasar France, Little Simz daga kasar Ingila, Nasty C daga kasar Firka ta Kuda da Tory Lanez daga kasar Kanada.
A
lokacin da ya hau kan mumbari domin karbar lambar yabon, Sarkodie yace “Ina so
in mika matukar godiya ga Ubangiji da iyali na kuma na sadaukar da wannan
lambar yabo ga ‘ya ta Titi…ina kyautata zaton cewa Afirka ta jima ana damawa da
ita kuma yanzu lokaci ya karato.Wannan lokacin mu ne kuma ina kira da babban
murya kowannen ku, ya koma gida domin duk wanda ya bar gida, gida ya bar shi”.
Comments