Watan yayin da daya daga cikin masu
sarrafa irin wadannan kidan mai sunan Kiddominant ya rantama hannu da kamfanin
Sony Music West Africa.
Kiddominant
mai shekaru 27 ya samu lambobin yabo da dama inda ya kware wajen sarrafa
wakokki salon Afro-pop. Yayi aiki da mashahuran mawaka irin su Davido, Wizkid,
Beyonce, Chris Brown, Wale, AKA, Rae Sremmurd, Mayorkun, Mr Eazi da Popcaan.
Tun
lokacin da ya sa hannu da Sony/ATV a
watan Maris na 2017, Kiddominant ya kara samun daukaka a irin salon
ayukan da yake saka. Shi ya sarrafa aikin Davido mai taken Fall wanda wakar ta
zamto babban bakandamiyyar wakar Davido inda wakar ta samu lambobin yabo da
dama wanda aka saka a wannan shekarar.
A
cikin shekara 2019, ingantaccen tushe ya nuna da cewa babban makaddin zamani ya
fito a cikin aikin kundin fefen Beyonce a karo na 7 mai taken B7, wanda ya nuna
da cewa wakar Nefertiti wanda aka rera tare da Rihanna, Kiddominant shine wanda
yayi aikin.
Sir
Banko wanda shine shugaban Sony Music West Africa ya bayyana wa manema labarai
cewa zasu bai wa kiddominant duk gudumawar da yake bukata wajen ganin an samu
biyan bukata.
Comments