Masu shirya babbar bikin daraja
mawaka wato “The Headies” a ranar 1 ga watan October sun saki jerin sunayen
wadanda zasu karbi lambar yabo a shekarar 2019.
Masu
shiryawa sun bayyana cewa akwai rukunoni 23 wanda za’a tantace mawaka wanda
suka samu shiga daga watan Januaru na shekarar 2018 zuwa watan Yuli na shekarar
2019. Wannan shine karo na 13 wanda za ayi mai taken “Power of a dream” wato
“Ikon mafarki” wanda za ayi a ranar 19 ga watan October, 2019.
Burna Boy shi yafi kowa fitowa a cikin rukunoni
takwas wanda suka hadu da rukunin Headies Viewers Choice, Song of the year
(wato waka ta shekara), Artist of the year (mawaki na shekara), Album of the
year (kundin fefen shekara), Best Collabo (wakar gamayya da tafi tasiri), Best
music Video (bidiyon da yafi fice), Best R&B/Pop Album (Fitaccen kundin
fefen R&B ko Pop), Best pop Single (wakar salon pop wanda tafi fice) da
Best Recording of the year (wato bakandamiyar wakar da tafi samun karbuwa
acikin al’umma).
Mr Eazi, Teni da Burna Boy sun fito cikin jerin wadanda zasu lashe lambar yabo na The Headies 2019 |
Comments