Shahararan
mawakin kasar Amurka Rick Ross ya samu karuwa a yayin da budurwar sa ta haifi
da namiji. Wannan shine dan sa na biyu da Brianna Camille. Amma abun mamakin
shine sunan da ya baiwa dan sa, Billion. Cikakken sunan dan nasa shine Billion
Leonard Roberts. Haka Rick Ross ya sanar a shafin sa na Twitter.
“Ku taya ni farin cikin zuwan da
na Billion Leonard Robert duniya” a cewar Rick Ross.
Mahaifin ya nan yana ta
shirye-shirye don ganin cewa dan nasa ya samu duk abun da yake bukata na
walwala a duniya. Rahotani yayi nuni da cewa Rick Ross ya biya bashin da
hukumar IRS ke bin sa na dalla miliyan daya, cikin bashin dalla miliyan shida wanda suke bin sa.
Wannan zabin sunan bai yi wa wasu
dadi ko kadan ba, musamman a dandalin Twitter. Wasu sun mayar da martini ganin
cewa ya Rick Ross zai bai wa dansa sunan da ke da alaka da kudi?
Kowa dai da kiwon da ya karbe
shi. Masu salon Magana sun ce abincin wani guban wani.
Comments