Mawakin
kasar Amurka wanda ake walakabi da Sarkin R&B wato R Kelly ya fada cikin
tsaka mai wuya a wannan lokacin a inda ake zargin sa da laifuka wadanda suka
shafi fyade ga mata masu karancin shekaru. Wannan ya biyo bayan da aka saki wani
labarin fim mai taken Surviving R-Kelly Docu-series.
Gajeren fim din da aka saka ya nuna
yanda shi mawakin yake tafiye da al’amurorin sa a duniyar waka, amma mawakin bai
taba kallon wannan fim din ba, a sannarwar da ya yi wa manema labarai.
A cewar jaridar TMZ, R.Kelly yana
aiki karkashin RCA Records wanda ke karkashin Sony Music. Kamfanin RCA sun
dakatar da sakin sabbin wakokin mawakin sai baba ya gani. Ko da dai R.Kelly
yana da wa’adin sakin kundin fefen ayuka har guda biyu a karkashin su, wasu
wadandan suka roka a sakaye sunan su sun ce baza su kasha wasu kudadde nan gaba
a kan ayukan sa ba sai an gama binkicen da ake yi a kan R Kelly a jihar ta Georgia.
Wannan matakin da RCA ta dauka zai
hanna R.Kelly cin moriyar samun kudadden shiga ta bangaren wakokin da ake
saurara a shafukan yanar gizo da sauran manhajjan da ke kan wayoyyin hannu.
Masoyan R.Kelly da allamu na nunin cewa basu da ra’ayin daina ji ko saukar da
wakokin sa. Kididdiga ya nuna cewa masoya da daman a dandazon sauraran wakokin
sa.
Kundin fefen R.Kelly wanda ya saka
daga karshe a karkashin RCA shine The Buffet – wanda shi ne aikin da R Kelly ya
taba saka wanda ya fi samun karancin kudaden shiga da kuma karbuwa daga masoyan
sa.
Kundin fefen R.Kelly kenan mai taken The Buffet |
Comments