Missy
Misdemeanor Elliot tana dab da ajiye wani babban tarihi a mazaunin mawakiya
mace ta farko wanda za a shigar da sunan ta cikin babban marubutan kasidu wanda
aka fi darraja a cikin shekarar 2017, wanda Associated Press suka rubuto.
Bayan da irin nasarorin da ta
samu a fannin salon hip-hop da pop, wato wakokin zamani, irin su Get ur freak
on, da wakar Lady Marmalade wanda ta rera tare da mawaka irin su Christina
Aguilera, Pink, Lil Kim da Mya, wanda wakar ta shafa shekaru da dama ana
saurarar ta, Mawakiyar da take rike da lambar yabo na Grammy za ta iya zama mawakiyar salon rap na uku
wanda aka taba karama da wannan babbar lambar.
Za ta zauna kujera daya da
mawaka biyu wanda su kacal aka bawa wannan lambar wato Jay Z da Jermaine Dupri
Mawakan da suka dau tsawon lokaci
wajen rubuta wakokin da suka yi fice, akalla shekaru 20, irin su ne suka
cancanta a baiwa wannan lamba na girmamawa. Missy Elliot dai ta yi aiki da
mawaka da dama irin su Timberland, Aliyah, Ginuwine, Destiny’s Child, Whitney
Houston da Ciara.
Missy Elliot ta zamo jajirtaciyya
don irin gudumawar da take bayarwa a fagen waka da irin salon basirar da take
amfani da shi a bidiyoyin ta.
Comments