LL
Cool J yana daya daga cikin wadanda suke shirye-shiryen wajan karawa da juna
don siyar gidan talabijin 22 sports channel
wanda aka tilasta wa Disney su siyar, kuma Ice cube ya nuna ra’ayin
siyar kamfanin.
A cewar jaridar TMZ Sports,
Disney sun siye tashar ne bayan wani yarjejeniyar da suka kulla da 21st
Century Fox. Disney su ke da hannun jari mafi rinjaye da kamfanin ESPN, kuma
siyan kamfanin zai zamo cewa zasu iya mallakan sauran gidajen talabijin 22 da
ke karkashin su, wanda zai basu daman mallakar kasuwar dungurungun.
Yarjejeniyar zai kai kimanin
dalla miliyan 15 zuwa 25. Sa’an da mawakan biyu ke da ita shine akwai wata
hamshakin mai kudi wanda take da ra’ayin siyan kamfanin wato Caroline
Rafealian. Sauran yan kasuwan da suke son siyar kamfanin sun kunshi Apollo
Global Management, Blackstone Group da Sinclair Broadcast Group.
Idan LL Cool J da Ice Cube suka
samu nasara, wannan zai basu daman mallakar tashoshin FoxSports San Diego,
FoxSports Arizona, FoxSports Detroit da FoxSports SouthWest da dai sauran su.
Comments