Bayan da daya daga cikin kungiyar BlackEyed Peas tayi murabus,wato Fergie, mutane da dama na alwashin cewa kungiyar baza ta cigaba da sakin sabbin wakokin da zasu yi tasiri ba.
Amma sauran yayan kungiyar basu bar wannan raunin ya dame su ba a inda suka cigaba da nuna jajircewar su da kara kulla dankon zumunci mai karfi a tsakanin su.
Nan take suka tuna da baya a yayin da
suka gayyaci daya daga cikin goggagun mawakan hip-hop, wato Nasir Jones wanda
aka fi sani da Nas domin fito da wani sabuwar aiki mai taken Back to Hip-hop.
Sabuwar wakar Black-eyed Peas mai taken Back To Hip-hop |
Tabbas kungiyar ta
Black-Eyed Peas basu gaza a cikin wannar aikin ba domin kuwa sun saki sabuwar kundin
fefen wakar su mai taken Masters Of The
Sun.
Sabuwar Kundin fefen Black-Eyed Peas kenan |
Comments