Wasikar Obasanjo: PDP ta mayar da martani ga Buhari da APC
A wasikar da tsohon Shugaban ya fitar ranar talatar nan data gabata, Wanda ta bazu a kafafen yada labarai, ya shawarce shi akan kada ya fito takara a zabe mai zuwa na shekarar 2019.
Ya kara da cewa, shawarar da Obasanjo ya bayar, ita ce zata fito da halin da jama'a suke ciki na kaka na kayi, da kuma tsarin demokradiyya a kasar nan. Jam'iyar tace yanxu tana nan akan bakanta na tsarin demokuradiyya, da kuma wakiltar jama'a ba tare da zalunci ko nuna kabilanci ba."Wannan shine dalilin da ya sa jam'iyyarmu zata kara zage dantse fiye da yanda tayi a baya, sannan zamu zo da sababbin manufofi wanda 'yan Nijeriya zasu bamu haÉ—in gwiwa." Yace, 'yan Najeriya sunyi tunanin Buhari shine mafita a gare su a zaben daya gabata na 2015, amma dai yanzu gaskiya ta tabbata. "Wannan dalilin ne yasa tsohon shugaban kasar ya bawa 'yan Najeriya shawara akan su lura da cancantar mutum kafin zabe".
"Saboda haka muna kira ga 'yan Nijeriya, ciki har da shugabanninmu a kowane bangare, su taru don sake gina al'ummar mu a kan tsarin da aka tsarin Jam'iyar PDP".
Comments