Daya daga cikin jaruman farko na masana'antar dake shirya fina-finai hausa Bashir Bala wanda aka fi sani da Ciroki ya sanar cewa ba buya yayi ba, masu shirya fim ne suka manta dashi.
Hirar shi da wakilin gidan watsa labarai ta BBC hausa,fitaccen dan wasa wanda yayi kaurin suna a da ya bayyana dalilin da ya sanya aka daina ganin shi a fina-finan.
Tsohon jarumin ya bada amsar tambayar da aka yi mai ta,dalilin da ya sanya aka daina ganin fitowar shi a fina-finai kamar haka;
"Ina nan ba buya na yi ba. Ka san shi wasa, ko kuma in ce fim, ba mutum shi yake daukar kansa ya jefa inda yake so ba.
"Akwai masu bayar da umarni, kamar abin da ake nufi koci a filin ball. Toh su ne suke da ra'ayin idan sun shirya fim, su dauko ka su sa ka.
"Yauwa. To ko ka iya ko baka iya ba , akwai wani ra'ayi nasu, da masu bayar da umarni da masu shirya fim, za a iya daukar ka a ajiye ka a kan benci sai bal ta zo karshe, mai yiwuwa in Allah Ya taimake ka sai a tuna wannan bal din fa babu wanda zai iya cin ta sai wane. Sai a dauko ka sai a saka.
"Misali zan maka. Ai mutane suna ganin kaman ba ma nan, ko kuma a'a mun ja baya ne kokuma yanzu ba mu iya ba.
"Toh salo ne da taku ya sauya na harkar wasanni. Na farko akwai jari hujja. Duk aktan da ka ga ana yawan ganinsa yana da jari ne a hannunsa.
"Zai iya fim nasa na kansa. Toh ka ga wannan ba za a iya cewa ya yi 'difom' ko kuma a'a basiarasa ta kare an daina yayinsa ba. A'a. Ba a daina yayin dan wasa ko wane iri ne.
"Sai dai idan daraktas ba sa ra'ayinsa za su iya ajiye shi, sai lokacin kuma da suka ga tunaninsu ya dawo kanka.
"Kamar yanzu Hajiya Balaraba Ramat Mohammed tana daya daga cikin wadanda suke kokartawa manyan aktoci da ake ajiyewa, ta shirya wani fim.
"Toh, role din da ma ta yi niyyar ba ni, ba shi aka ba ni ba daga farko, amma daga karshe sai aka zo aka zauna aka ga a 'to ai akwai munfunci a fim din, tun da ga Ciroki ya kware a wajen, a zo a gwada shi mana."
Ciroki wanda ya shahara a fagen barkonci zai taka rawa a wani sabon shiri mai take "juyin Sarauta".
Comments