Skip to main content

Labari: An gafarta wa jaruma Rahama Sadau




Hukumar tace fina-finan hausa ta yafe ma fitacciyar jaruma Rahama Sadau bisa laifin da ta aikata wanda yayi sanadiyar har aka dakatar da ita da yin fim.

Shugaban hukumar Isma'ila Na'abba Afakalla ya shaida wa wakilin BBC haka.

Shugaban yace an dauki matakin ne bayan gafarar da jarumar ta nema kwanan baya.

"Wannan baiwar Allah ta zo ofishina a shekarar da ta wuce inda ta nemi gafara kan abubuwan da ta yi a baya; na gaya mata ta je ta nemi gafarar Gwamna da Sarkin Kano kuma ta fito a gidan rediyo ta nemi afuwarsu da ta al'umar da take ciki".

"Don haka a matsayinmu na 'yan-Adam wadanda kullum muke cikin kuskure, so muke a ja mutum a jiki kada ya fandare, shi ya sa muka yafe mata. Duk lokacin da mutum ya yi laifi ba a rufe masa hanyar tuba. Kuma ko yanzu ta kawo fim za mu tace shi".

Afakallah ya sanar cewa "A shirye muke mu soma tace fina-finan da za ta rika fitowa a ciki da kuma wadanda take daukar nauyinsu".











Jaruma ta bada hakuri
Rahama Sadau ta nemi gafara ne bisa kuskuren da tayi na rungumar wani mawaki a cikin bidiyon wakar shi.

A cikin watan Octoba na bara Fitacciyar jarumar ta bada hakuri ga gwamnan jihar kano da mai martaba sarkin kano da mabiyan fina-finan kannywood ne a wata hira ta musamman da tayi a shirin "ku karkade kunnuwan ku" wanda gidan rediyo na Rahama dake nan jihar Kano ke gabatarwa.

Bayan haka ta tura wasikar neman gafara ga kungiyar wanda har sakataren kungiyar Muhammed Salisu ya tabbatar da isowar wasikar ga farfajiyar kungiyar.

A cikin wasikar tana mai cewa; "Ni halittar Allah ce wanda za ta iya aikata kuskure ko yaushe sannan kuma ni ‘ya ce mai laifi wanda ke shirin gyara abubuwan da nayi ba daidai ba. Ina rokon abokan aikina, da mambobin kungiyar masu MOPPAN, da da masoya na da suyi hakuri da ni su yafe min".

Yanzu haka jarumar tana kasar Cyprus inda take karatu kana tana kokarin fitar da wani sabon fim wanda ta dauki nauyin shiryawa mai take "Dan Iya".

Shirin wanda shine na biy da zata dauki nauyin fitarwa bayan RARIYA zai fito nan ba da jimawa ba.

Comments

Popular posts from this blog

BILLY O - KATAKO

After remaining a legend in the music game for more than a decade, Billy O finally release the smashing single titled KATAKO. KATAKO is a song with a mixed meaning. Though Katako means Timber in English language, this song is more of  a proverbial song that has a deep meaning lying in it. The afro-centric rhythm of the song will make you love the unique style re-created by BILLY O and as a matter of fact, he knows how to deliver when he meets the best. Produced by Nexcezz Beatz, download and listen to this sumptous tune by BILLY O titled KATAKO . BILLY O - KATAKO mp3

RICQY ULTRA -TSAYA KAJI

RICQY ULTRA IS ONE OF THE FEW EMCEES IN KANO CITY WHO ARE STICKING THEIR GUNS TO THE REAL HIP-HOP CULTURE. AFTER CHURNING AND DROPPING SINGLES, MIXTAPES AND VIDEOS PORTRAYING THE VIBRANT HIP-HOP CULTURE IN NORTHERN NIGERIA, HE UNLEASHES THIS BRAND NEW JOINT TITLED "TSAYA KAJI" . "Tsaya Kaji" is a Hausa word which means "Just Listen" is a strong hip-hop sound that has a deep energy. The song is a conscious rap song which resonates elements like boldness, courage, envy, hate, pain and authority. The lyrical delivery from verses laid in the song tells a lot of story. Verse 1 of the song tells a story about how the patient ones are being taken for granted and treated like slaves, how you can hardly trust friends and  everyone around you is so unpredictable. Verse 2 summarises a tale of a young boy whose parents are poor and visibly sick. He left them for Almajiranci to Kano city to hustle only to meet people with the same fate as he. What next? ...