|
Masoyar Gwaska Returns |
Shaharrren dan wasan kwaikwayon Kannywood Adam A Zango, ya karrama masoyan sa dake garin Kano a lokacin bukin shirrin kaddamar da sabuwar fim din sa mai suna gwaska Return da zai fito a ranar 1 ga watan Janairu na shekara 2018.
|
Jarumi Adam A Zango tare da masoyan sa |
Jarumai kamar Ali Nuhu, Nafisa Abdullhi Fatu SU, Ado Gwanja, Nura M. Inuwa, Fati Abubakar da dai sauran manyan jarumai da masoya sun halarci bikin a Film House Cinema dake Ado Bayero Mall a babban birnin Kano.
|
Kungiyar White House Family a wajen taron |
|
Tijanni Asase tare da jaruma Nafisat Abdullahi |
Daya daga cikin hadiman Zango, mai suna Mansur Make-Up, ya bayyana wa yan jarida cewa Adam Zango ya shirya bikin ne domin nuna wa masoyar sa irin kaunar da yake musu.
|
Daya daga cikin masoyan Gwaska Returns |
Jaruma Fati S.U ta shaidawa yan jarida cewa Adam Zango mutum ne mai matukar kaunar jama’a, kowa nasa ne, kuma abun da yayi wa masoyan sa abun ne da ya cancanci yabo ne. Mutum ne dake da matukar kyauta da taimako. Har mu ma jaruman fim bai bar mu wajen ganin cewa mun samu daukaka a masana’artar fim.
|
Horo Dan Mama tare da wata masoya a wurin taron |
|
Wurin taron kamun a fara shigowa |
Adam aZango ya ba da kyaututuka da dama daga riguna, huluna, agogo da dai sauran su. Bayan haka kuwa, ya karama wasu masoyar sa a wurin bikin.
Comments