Nazir M Ahmad zai kai gidan talebijin kara kotu a kan miliyan 100 don amfani da fasahar sa ba tare da izini ba
Nazir M. Ahmad ya bukaci gidan talebijin da biyan diyar N100M kan amfani da wakar shi ba tare da izinin shi
"Suna amfani da ita bada izinina ba kuma mun nemi su fada mana dalili sun yi shiru, shine muka ce za mu bi hanyar da ta dace domin karbar hakkinmu" a cewar mawakin.
Shahararren mawaki hausa Nazir M.Ahmad ya nemi wani gidan telebijin da ta biya diyar naira miiliyan dari (N100M) kan amfani da wakar shi da suka yi a wata fim da suka fitar ba tare da sun nemi izinin shi.
A bisa labarin da Rariya ta wallafa a shafin ta na Facebook, mawakin yace Ebonylife tv tayi amfani da wakar sa mai suna "Bincike" a cikin shirin Sons of the caliphate ba tare da sun nemi izinin ba kuma da ya tuntubi su game da dalilin da ya sanya suka aikata haka amma sunyi shuru.
Nazir Sarkin waka yace sanadiyar haka ya zai bi hanyar da doka ta amince dashi wajen kwato hakkinsa kuma lauyoyin sa sun tura masu rubutu game da lamarin.
"suna amfani da ita bada izinina ba kuma mun nemi su fada mana dalili sun yi shiru, shine muka ce za mu bi hanyar da ta dace domin karbar hakkinmu." yace.
Mawakin wanda yace ya tanaji duk wani hujjan da kotu ke bukata ya kai karar su kotu kuma ya bukaci su da biyan shi domin doka ta bashi damar yin haka.
Pulsehausa ta tuntubi gidan telebijin game da zargin da mawakin yake yi amma sunyi kunnen doki game da lamarin inda suke cewa basu da labarin haka.
A bisa rahoton, mawakin yace baya sakaci game da ayyukan shi na fasaha shiyasa yaike masu dokar hakkin mallaka kuma lokaci kawai suke jira domin gabata a gaban kotu.
Daga karshe ya baiwa sauran abokanan sana'ar shi shawara da su kula da duk abinda ya shafe su ta hanyar mallakar hakki domin zai taimaka wajen kare mutuncin hakkin kayan su.
**An dago labarin nan daga shafin Pulsehausa.
Comments