Fittaciyar jarumar masana'antar Kannywood Maryam Booth ta mayar ma wata ma'abociyar shafinta da martani mai radadi bisa ga bakan maganar da tayi.
Lamarin ya faru ne sanadiyar sakon talla da jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram na wata garabasa da Jaruma empire wanda ke safarar kayan ma'aurat ke bada wa ga kustomomin ta.
Sako ne ga duk mai son samun garabasa amma wata mai suna @fadeelamatawalle mai bibiyan shafinta tayi mata mummunar fassara.
"Allah ya kyauta ya shirya ki. Ashe duk irin ku daya ne. koda yake yanzu nagan Allah ya fara shiryata tanasa dan mayafi. Jaruma mai naira kuma mai kyautar nairori ashe tana baki kudi?. Ashe kina amsan kaya shiyasa kika kasa aure duk da gorontulan da lakanin nata". ta rubuta.
Sakamakon abun da ta rubuta jarumar ta mayar mata da martani kamar haka; "@fadeelamatawalle Baki da labari? @jaaruma_empire tana bani kudi kam ba karya.
@fadeelamatawalle Allah sarki gaki yarinya karama sai uban Shishigility but I don’t blame u I blame tsohuwarki da bata baki tarbiyar “mind ur business ba” ur too young for all this and inkinji haushin rashin aurena DM me ur fathers number".
Bayan wanan cece kuce tsakanin Maryam Booth da mabiyan shafin ta ya faru wasu suka gan cewa abun bai dace ba. Ga abun da wata daga cikin mabiyan ta ta rubuta.
@leema_maitama ta ce "Haka kawai ku kama yarinya da zagi harda ubanta, ai celebrities ba haka suke ba ansansu da hakuri da juria dakuma kawarda ido akan kome zaa gaya musu ki kiyayi bakin dunia @officialmaryambooth".
Comments