Babban É—an tsohon shugaban jam'iyar PDP Bilyaminu Muhammed Bello ya mutu bayan matar sa ta caka masa wuka har sau uku bisa ga wannan dalilin....
Lamarin ya faru a gidan su dake Wuse 2 nan garin Abuja a safiyar ranar lahadi 19 ga watan nuwamba
Maryam Sanda wanda diyyar tsohuwar mai ruwa da tsaki na bankin Aso Savings ce ta kashe mijin ta Bilyaminu bisa ga zargin cewa yana nema ya kara aure.
Ta neme shi da fada bayan wani sako ta waya da ta gani a wayyar shi tsakanin shi da wata da take zargin cewa sabon maso'iyar shi ce.
Majiyar mu yace tun kafin lamarin ya faru ne Bilyaminu ke fuskantar matsala daga uwardakin sa domin tasha ji masa rauni kan zargin yana neman mata.
Babban abokin marigayin mai suna Mustapha Dikko ya shaida ma manema labarai cewa a ranar da Maryam ta kashe mijin ta, sun samu tsabani ne inda ta bukace shi da ya sake ta. Bayan kai-kawo da suke tayi ne ta caka masa wuka a kirjin sa har sau uku.
Karanta inda wata tayi sanadiyar rasuwar mijinta bayan tayi masa karya. Ita da kanta ta kaishi asibiti bayan laifin da ta aikata amma likitoci basu samu damar ceci rayuwar shi.
Ma'aikatar asibitin sun sanar ma hukumar yan sanda lamarin kuma hukumar tace ana bincike akan lamarin.
A zaman auren su wanda ya kai kimanin shekara biyu, Maryam da bilyaminu sun samu É—iya yar wata takwas.
Comments